A cikin jerin wasikunmu na 'yan jaridar Afirka, marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani, ta yi duba kan korafe-korafen ma'aikatan lafiyar da suka ceto Najeriya daga fadawa cikin bala'in annobar Ebola a shekarar 2014, wadanda suka yi aiki tukuru amma har yanzu ba a biya su hakkokinsu ba.
A watan Oktobar 2014 ne Najeriya ta samu yabo a duniya kan yadda ta yi gaggawar dakile yaduwar annobar cutar Ebola, wadda ta yi barna sosai a makwabtanta da ke Yammacin Afirka kamar su Saliyo da Guinea da Laberiya.
Amma tuni likitocin babbar tawagar da suka yi wannan hobbasa na Cibiyar Kare Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC, suka bar aikinsu, saboda an ki biyansu albashinsu na kusan shekara uku.
"Idan da za su iya dawo da hannun agogo baya, ba za su neme ni don na yi aikin nan ba," in ji Dr Kenneth Madiebo, wani likita mai shekara 53 da ya kula da gawar Patrick Sawyer, wanda shi ne mutum na farko da aka gano yana dauke da cutar Ebola a Najeriya a shekarar 2014.
Dr Madiebo wanda jami'i ne a cibiyar NCDC tun watan Satumbar 2012, an sanya shi aikin kawar da duk wani abu da zai iya yada cutar daga dakin asibitin da Mista Sawyer ya mutu a watan Yulin 2014, kuma shi ne ya kintsa gawar mamacin don a konata.
A wani bidiyo da ya nuna min, Dr Madiebo, wanda shi ne kadai jami'in lafiyar da ya yi wannan hobbasa, ya jagoranci masu kula da gawa wajen ciro gawar Mista Sawyer daga wani da tsukukun ban-daki inda a nan ne ya mutu.
A tabbatar da mutuwar Mista Sawyer tun karfe 7:30 na safe amma ba a ciro gawarsa ba sai karfe 11:30 na dare.
Dr Madiebo ya ce: "Kowa yana jin tsoro, ba wanda yake son yin wannan aiki. Amma ni na yi saboda aikina ne."
"Na yi rashin lafiya kwanaki kadan bayan hakan, amma na san firgici ne kawai ba Ebola ba."
Ya samu yabo daga wajen mutane a yayin da aka sanar a hukumance cewa babu Ebola a Najeriya a ranar 20 ga watan Oktoba, bayan nan kuma ministan lafiyar kasar a wancan lokaci Onyebuchi Chukwu, ya umarci Dr Madiebo ya mike tsaye a yayin wani taron manema labarai, inda ya jinjina masa tare da yabonsa a gaban mutane kan rawar da ya taka ta dakile yaduwar Ebola.
A wannan watan ne kuma dai ministan ya yi murabus daga mukaminsa don tsayawa takarar siyasa, a yayin da shi kuma Dr Madiebo ya samu ci gaba a aikinsa, matsayin da ya sa yawan albashinsa ya karu.
Amma fa tun daga wancan lokacin har zuwa yau ba a sake biyansa albashi ba, walau sabon ko tsohon.
Wata abokiyar aikinsa Colette Isu-Ezumah, mai shekara 43, wadda ta koma Najeriya daga Amurka a shekarar 2011, ta bani labarin irin wannan tagayyara.
Ita ce kashin bayan hada wannan tawagar ta masu aikin sa-kai 'yan Najeriya 250 da aka tura Saliyo da Laberiya domin su taimaka wajen yaki da Ebola, a yayin da cutar ke kan ganiyar yaduwarta a shekarar 2014 da 2015.
Baya ga wannan, kuma dai kamar yadda ya faru ga Dr Madiebo, ita ma Ms Isu-Ezumahba a biyata albashi ba tu watan Oktobar 2014.
"Shugabanmu ya sha gaya mana cewa ka da mu damu, za a biya mu,: in ji ta.
Da ya gaji da gafara sa bai ga kaho ba, sai kawai Dr Madiebo ya dauki hukunci a hannunsa.
A wannan lokaci ba a dade da zabar Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar ba, kuma da yake ba a saka sabon minista a ma'aikatar lafiya ba, sai babban sakatare Linus Awute ya zama shi ke jan ragamar.
Dr Madiebo ya aikawa Mr Awute sakon email, tare da sanya sunan abokan aikinsa shida wadanda su ma ba a biya su albashi ba tsawon wata tara.
Amma a amsar da Mr Awute ya aikawa Dr Madiebo sai ya ce: "Baka da damar da za ka turo min sakon email kai tsaye, bayan ka san cewa kana aiki ne karkashin mutane da dama a ma'aikatar lafiya ta kasa."
"Ina wannan hali na rashin da'a da rashin ladabi ya samo asali?"
Ya kara da cewa: "A iyakar sanina, tsarin biyan albashinka yana karkshin wata doka ce ta ma'aikatar lafiya ta kasa.
"Kuskure daya a nan shi ne ma'aikatar lafiya na bukatar dakatar da kai na dan wani lokaci saboda wannan sakon email din naka mai cike da rudani.
Source: BBC Hausa
Title :
Haryanzu Ba'abiya Likitocin Dasukayi Yaki Da Ebola Ba
Description : A cikin jerin wasikunmu na 'yan jaridar Afirka, marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani, ta yi duba kan korafe-korafen ma'aikatan lafiyar ...
Rating :
5