Ministan wasanni a Najeriya, Solomon Dalung ya ce babbar matsalar da gwamnatinsu ke fuskanta ita ce abin da ya kira "guguwar Buhari".
"Wannan guguwa ta kwaso mana su mesa, su damo, kura da su kunama, kuma yanzu kowa ya fara fitar da halinsa.
Tafiya ce ta hadin gambiza dmon Dalung na wannan jawabi ne lokacin da yake zantawa da BBC don mayar da martani ga sukar da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya yi wa Buhari a baya-bayan nanke da shi ne ke hana mutane irinsa gaBuhari.
Ministan ywanko wani karin magana da ke nuna cewa sai dai kare ya mutu da haushin kura, saboda "suna da niyya ya ba su wuri, don haka babu wani abu mai kyau da zai yi su gani".
Ya ce kafin zuwan gwamnatin Buhari, akwai shingen binciken sojoji fiye da ashirin daga Abuja babban birnin kasar zuwa Jos, don haka sai ka shafe tsawon fiye da sa'a biyar a wannan tafiya.
"Akwai kananan hukumomi wadanda suka fi ashirin suna karkashin 'yan kungiyar Boko Haram da tutarsu a wuraren. Yanzu haka babu. Mun karbi Najeriya, mun mika a hannun 'yan Najeriya."
"Idan ana maganar yaki da amubazzaranci, wai (suna cewa) ba a samu ci gaba ba. Adadin kudaden da aka karbo, a nuna tarihin Najeriya, gwamnatin da ta yi irin wannan kokari."
Ya shawarci Atiku Abubakar ya je kai tsaye ya gana da shugaban kasar idan yana son ba shi shawara maimakon kwarmata gazawar gwamnatinsa a bainar jama'a.
"Idan har dattijo ya kai magana gidan rediyo, to kenan yana da buri, yana nuna cewa yana da burin sarauta (mulki) shi ya sa ya kai magana bainar jama'a."
Dalung ya yi ikirarin cewa babu wani jigo a jam'iyyar APC da zai bukaci ganawa da Muhammadu Buhari, amma shugaban ya hana shi dama.
"Buhari ba mutum ne da yake da shinge ba, sam babu."
Source: BBC Hausa
Title :
Guguwar Buhari Ne Babbar Matsalanmu-Dalung
Description : Ministan wasanni a Najeriya, Solomon Dalung ya ce babbar matsalar da gwamnatinsu ke fuskanta ita ce abin da ya kira "guguwar Buhari&quo...
Rating :
5