Gobara ta hallaka wasu dalibai 'yan mata bakwai a babban birnin Kenya, Nairobi, bayan da wuta ta kama dakin kwanansu na makaranta a cikin dare.
An kwantar da wasu 16 a asibiti yayin da wasu sama da dubu daya suka tsira daga gobarar ba tare da wani rauni ba, sa'ilin da ake ci gaba da kokarin gano abin da ya haddasa wutar.
Ana ganin wutar ta tashi ne da misalin karfe biyu na dare a ranar Asabar, a makarantar 'yan mata ta Moi Girls' School, a lokacin daliban na barci.
Ba tare da wani jinkiri ba 'yan kwana-kwana suka kai dauki, amma kuma duk da haka kafin su iso lamarin ya riga ya rutsa da wasu daga cikin 'yan matan.
Gwamnati ta rufe makarantar tsawon mako biyu domin gudanar da bincike kan abin da ya haddasa gobarar da kuma yadda har ta hallaka daliban.
A shekarar da ta wuce an rika samun gobara nan da can a daruruwan makarantun kasar a cikin wata uku, lamarin da aka dora a kan bata gari da ke cinna wutar bisa wasu dalilai na kashin kansu.
Akwai korafin rashin samar da matakan kare lafiya da suka dace ba a makarantaun kasar ba kadai har ma da sauran gine-ginen gwamnati da dama a Kenya.
Source: BBC Hausa
Title :
Gobara Ya Hallaka 'Yan Mata Bakwai A Kenya
Description : Gobara ta hallaka wasu dalibai 'yan mata bakwai a babban birnin Kenya, Nairobi, bayan da wuta ta kama dakin kwanansu na makaranta a ciki...
Rating :
5