A kalla dalibai 24 da malaman makaranta ne suka mutu a sakamakon wata gobara da ta tashi a wata makarantar islamiyya a Kuala Lumpur, babban birnin kasar Malaysia.
Gobarar ta tashi ne a Makarantar Tahfiz Darul Quran Ittifaqiyah da safiyar Alhamis.
Ana zaton wadanda suka rasu din wutar ta rutsa da su ne a ɗakunan kwanansu, yayin da tagogin suke a rufe da karafan da aka sa don ba da tsaro .
Darekta na sashin kashe gobara da ayyukan ceto, Khirudin Drahma, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "Yana daya daga cikin mummunan bala'i da ya faru a cikin shekara 20 da suka gabata."
Da farko an kirga yawan wadanda suka mutu a matsayin 25, amma 'yan sanda suna sake nazarin yawan mamatan.
'Yan sanda sun ce 'yan makarantar da suka rasu su 22 ne - dukkan su yara maza ne tsakanin shekaru 13 da 17 - da kuma ma'aikata guda biyu.
An kai mutum goma zuwa asibiti, kuma ana zaton hudu sun samu mummunan rauni.
An bayar da labarin cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 05:40 na safe agogon kasar a ranar Alhamis. 'Yan sanda sun ce wutar ta fara ne tun cikin dare.
A Malaysia makarantun tahfiz na musulunci na yara, yawanci makarantun kwana ne.
Mataimakin darakta na hukumar kashe gobara Soiman Jahid ya ce: "Bisa ga bincikenmu na farko, mun gano cewa yaran sun yi kokarin guduwa amma karafun da ke jikin tagogin sun yi musu shamaki da hakan.
Ya ce 'yan sanda suna binciken abin da ya haifar da gobarar amma mai yiwuwa wutar lantarki ne ta jawo ko kuma maganin sauro.
Kafofin watsa labaran kasar sun nuna cewa watakila ba a bude makarantar bisa dokar gwamnati ba.
Minisatan gidaje da raya karkara na Malaysia ya ce an samu bala'in gobara wajen 29 a makarantun tahfiz a kasar tun 2015.
Hukumomi na Malaysia suna nuna damuwa kan rashin tsaro a makarantun islamiyoyi da aka bude ba bisa ka'ida ba.
A farkon wannan shekara an bayar da rahoton cewa, wani yaro dan makaranta dan shekara 11 ya mutu bayan wani malamin makarantar islamiyya ya yi masa duka.
Wani mutum da ke zama kusa da makarantar ya fadawa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa sun ji ihu kuma sun ga wuta na ci.
Ya ce "yaran suna ta kuka a taimake su, amma sai dai na kasa taimakawa saboda kofa ta riga ta kama da wuta.''
Babban jami'in 'yan sanda na Kuala Lumpur Amar Singh ya ce gawarwakin "sun kone kurmus".
"Cikin rashi sa'a kofar shiga daya ce, don haka suka kasa tsira, an samu gawarwakin cunkushe daya kan daya."
Jami'ai sun ce motocin kashe wuta sun kai wajen ne cikin lokaci kankani, kuma an kashe wutar a cikin awa daya.
Firai Minista Najib Razak ya aika sakon jajensa a shafin Twitter ga wadanda abin ya shafa, wani ministan gwamnati ya ce a yi sauri a gudanar da bincike alamarin saboda a kiyaye irin wannan bala'i a gaba.
Source: BBC Hausa
Title :
Gobara Takashe Dalibai Da Dama A Makarantar Islamiyya A Malaysia
Description : A kalla dalibai 24 da malaman makaranta ne suka mutu a sakamakon wata gobara da ta tashi a wata makarantar islamiyya a Kuala Lumpur, babban ...
Rating :
5