Wani limanin cocin katolika a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya bai wa wadansu Musulmi su 2000 mafaka lokacin da suke cikin fargabar fuskantar hari daga kungiyar gwagwarmayar Kristoci ta anti-Balaka.
Fasto Juan José Aguirre Munoz ya ce Musulmin 'yan gudun hijiran ba za su bar harabar cocinsa ba a birnin Bangassou da ke kudu-maso-gabashin kasar, sai bayan ya samu tabbaci kan tsaron rayukansu.
Ya ce Musulmin da ya ba mafaka suna "fuskantar barazanar kisa" ne daga wurin mambobin kungiyar anti-Balaka.
Wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Stephen O'Brien ya yi gargadin cewa akwai alamun aikata kisan kare dangi a makon jiya.
Ya ce rikicin kasar yana kara ta'azzara kuma al'amarin yana kara muni.
"Tashin hankalin yana karuwa, ana tsoron kada a kara maimaita mummunan rikicin da ya faru a kasar kimanin shekara hudu da suka wuce," in ji shi.
Mista O'Brien ya kara da cewa: "Akwai alamomin da ke nuna yiwuwar faruwar kisan kiyashi don haka wajibi ne a dauki mataki."
Source: BBC Hausa
Title :
Fasto Yakare Musulmai 2000 Cocin Sa
Description : Wani limanin cocin katolika a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya bai wa wadansu Musulmi su 2000 mafaka lokacin da suke cikin fargabar fuskantar h...
Rating :
5