Jarumar fina-finan Hausa, Hauwa Abubakar wacce aka fi sani da Hauwa Waraka, ta ce tana yawan fitowa a mutuniyar banza ne saboda ta nunawa al'umma illar rashin kirki.
"Ina fitowa a matsayin karuwa ko 'yar kwaya ko ballagaza ne saboda na ilimantar da mutane domin su guji zama irin wadannan mutane", in ji Hauwa Waraka, a hira ta musamman da BBC.
Ta kara da cewa, "Ban taba karuwanci ba kuma ban taba yin hulda da karuwai ba, amma idan ina taka rawa a matsayin karuwa kai ka ce ni tsohuwar magajiya ce."
A cewar jarumar bai kamata mace da za ta fito a matsayin karuwa "a gan ta sanye da hijabi ba. Ko kuma macen da ta fito a matsayin 'yar shaye-shaye a gan ta ras kamar mutuniyar kirki ba.
"Shi ya sa za ka gan ni ina keta rashin mutunci a fim kamar da gaske. Kuma abin da ya kamata kenan."
Hauwa Waraka ta ce sau da dama tana zuwa unguwa mutane suna "cewa wacce irin kwaya ko wiwi ko taba za su kawo min na sha. Ba su san cewa ban taba shan kayan maye ba; wallahi ko taba ban taba sha ba. Duk abin da ka ga ni a fim ne".
Da aka tambaye ta kan zargin da ake yi wa 'yan fim na luwadi da madigo, jarumar ta ce akwai bara-gurbi sosai a cikinsu "kamar yadda akwai su a cikin ko da Malaman addini amma bai kamata a yi mana kudin-goro ba
Ta bukaci mutane su rika yi musu uzuri musamman ganin cewa su ma mutane ne kamar kowa.
Hauwa Waraka, wacce ta ce tana son yin aure, ta kara da cewa "kai ma wakilin BBC idan kana sona ka fito. Wallahi aurena ba zai yi tsada ba. Kai, ni zan hada maka lefe ma akwati shida idan kana so.
"Ko da yake na san tsoron matarka kake yi kada ka je gida ta ki bude maka kofa"...(dariya).
Source: BBC Hausa
Title :
Dalilin Dayasa Akemin Kallon 'Yar Wiwi-Hauwa Waraka
Description : Jarumar fina-finan Hausa, Hauwa Abubakar wacce aka fi sani da Hauwa Waraka, ta ce tana yawan fitowa a mutuniyar banza ne saboda ta nunawa al...
Rating :
5