Ba sanya Diego Costa a cikin tawagar da za ta buga wa Chelsea gasar Zakarun Turai ba.
Dan wasan mai shekara 28 bai buga wa kungiyar wasa ba a kakar da muke ciki, kuma ya kwashe kusan dukkan watan Agusta a kasarsa Brazil.
Costa yace yana son komawa Atletico Madrid, saboda Chelsea na kallonsa tamkar "mai laifi" inda suke neman karbar kudin da wuya a biya a kansa.
An sanya dan wasan a cikin tawagar da za ta buga wa Chelsea gasar Premier bayan an rufe kasuwar musayar 'yan kwallon kafa, sai dai babu tabbas game da makomarsa a kungiyar.
A bangare guda, Manchester United ta sanya Zlatan Ibrahimovic a tawagarta da za ta buga gasar Zakarun Turai, ko da yake ba a tsammanin zai ji sauki daga jinyar da yake yi kafin watan Disamba.
Dan wasan mai shekara 35 ya fito sau 46 a wasan da kungiyar ta yi a kakar wasan da ta wuce sannan ya ci mata kwallo 28, yayin da kuma a watan Agusta ne ya sabunta kwantaraginsa da kungiyar tsawon shekara daya.
A cikin 'yan wasan da aka sanya a tawagar har da dan wasan tsakiya James Wilson, mai shekara 21, wanda rabonsa da buga wasa tun a watan Oktoban 2016 lokacin da Derby ta karbi aronsa kuma ba a ba shi lamba ba a farkon gasar Premier,ko da yake yanzu an ba shi lamba 29.
Liverpool bata sanya Nathaniel Clyne cikin tawagarta ba. Dan wasan na Ingila, mai shekara 26, yana jinyar ciwon baya tun farkon kakar wasa ta bana.
Ita ma Tottenham ba ta sanya dan wasan gaba Vincent Janssen cikin tawagarta ba.
Source: BBC Hausa
Title :
Chelsea Bata Sanya Costa A Yan Wasan Zakarun Turai Ba
Description : Ba sanya Diego Costa a cikin tawagar da za ta buga wa Chelsea gasar Zakarun Turai ba. Dan wasan mai shekara 28 bai buga wa kungiyar wasa ba...
Rating :
5