Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan al'amura da dama da suka hada da korafin da ya yi na watsi da shi da aka yi a tafiyar da harkokin gwamnatin.
A wata hira da gidan rediyon VOA Hausa, Alhaji Atiku ya ce jam'iyyar APC ba ta yi da shi duk kuwa da irin taimakon da ya yi wajen kafuwarta da gwagwarmayar da ya yi wajen ganin an kayar da jam'iyyar adawa ta PDP.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce: "Ina cikin jam'iyyar APC da ni aka yi yawo aka yi kamfe amma tun da aka kafata ba a sake bi ta kaina ba an mayar da ni saniyar-ware, ba ni da wata dangantaka da gwamatin, ba a taba tuntubata ko da sau daya don jin ta bakina a ko wacce harka ba, ni ma shi ya sa na janye jikina."
Kalaman nasa na zuwa ne kwana daya bayan da ministar harkokin mata a gwamnatin Buhari Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta shaida wa BBC cewa za ta goyi bayan Atiku ya tsaya takara a shekarar 2019 ko da kuwa Buhari zai tsaya.
Atiku ya kara da cewa: "Sun yi amfani da kudinmu da dukiyarmu da karfinmu wajen ganin sun ci zabe amma ga shi ana neman shekara uku ba abin da ya sauya."
Alhaji Atiku ya ce abin da kawai zai yaba wa Shugaba Buhari akai shi ne yaki da kungiyar Boko Haram, "duk da cewa wannan din ma ba a murkushe kungiyar gaba daya ba.
"Sai kuma yaki da cin hanci da rashawa amma wannan ma ba a yi wani abin a zo a gani ba tun da har yanzu ba a kai ga daure kowa ba."
"Ina iya tunawa a lokacin da muka karbi gwamnati a shekarar 1999, mun kwato dala biliyan 4.7 daga hannun jami'an gwamnatin Sani Abacha, kuma mun gaya wa al'umma.
Atiku ya kara da cewa, akwai matsaloli birjik da ke gaban jam'iyyar APC a gwamnatance da kuma a jam'iyyance, in da har yau ba a taba taron jam'iyya ba ko sau daya.
Ya kuma ce yanzu haka a Najeriya babu wada ba ya shan wahala daga bangaren 'yan arewa zuwa 'yan kudu kowa kokawa yake har da 'yan Biafra da bangaren Yarbawa, 'ba a taba shiga yanayi mai wahala irin wannan ba.'
Sai dai ya ce duk da ya san mutane suna ta neman ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekarar 2019, shi har yanzu bai gama ynake shawara ba sai zuwa shekara mai zuwa.
"Ni mutum ne da na tashi da so taimakon jama'a saboda na tashi cikin talauci na ga yadda ake shan wahala, yanzu ba lokacin tsayawa takara ba ne, burinmu talaka ya samu farin ciki tukunna," in ji Atiku.
Ko a ranar Laraba ma Alhaji Atiku ya soki gwamnatin Buhari inda ya ce akwai sauran rina a kaba kafin hukumomin kasar su tabbatar da an kawo karshen matsalolin da suka addabi tattalin arzikin da yaki ci yaki cinyewa a kasar.
Source: BBC Hausa
Title :
Buhari Yayi Watsi Da Wadanda Suka Taimakeshi-Atiku
Description : Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya caccaki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan al'amura da dama da s...
Rating :
5