Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce akwai sauran rina a kaba kafin hukumomin kasar su tabbatar da an kawo karshen matsalolin da suka addabi tattalin arzikin da yaki ci yaki cinyewa a kasar.
Ya fadi wadannan kalaman ne a shafinsa na Twitter, inda ya fara da nuna farin cikinsa da samun labarin fitar kasar daga kangin tattalin arziki.
Ya ce: "A matsayina na dan Najeriya, kuma mai zuba jari da daukar ma'aikata, labarin cewa Najeriya ta fice daga matsalar tattalin arziki abu ne mai faranta rai".
"Wannan labari ne da lallai zai daukaka martabar Najeriya - domin yana gaya wa masu zuba jari na cikin gida da na waje cewa tattalin arzikinmu na da karfin da za su cigaba da mu'amulla da shi".
Amma ya bayyana shakkunsa dangane da tasirin fitar Najeriya daga matsalolin da koma bayan tattalin arzikin ya janyo.
"Duk da muna farin ciki da wannan labarin, amma yana da muhimmanci mu lura cewa har yanzu marasa galihu na fuskantar matsalolin karyewar tattalin arziki. Har yanzu akwai hauhawar farshin kayan more rayuwa sosai", in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.
Atiku Abubakar ya yi kira da a kara kaimi wajen samar da dabarun ci gaban 'yan kasar masu karamin karfi: "Dole mu cigaba da aiki tukuru domin fadada hanyoyin wanzuwar tattalin arziki ga 'yan Najeriya."
Ya karkare sakon nasa da cewa: "Sai lokacin da dukkan 'yan Najeriya za su iya cin abinci sau uku a rana ne za a ce koma bayan tattalin arziki ya kare. Muna da sauran aiki a gabanmu".
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin ciki da farfadowar tattalin arzikin Najeriya, bayan dawowarsa daga jinya a birnin Landan.
Ya ayyana hakan ne bayan ya gana da Ministar Kudin kasar, Kemi Adeosun da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele.
Masana da yawa da suka hada da wani masanin tattalin arziki a Nijeriya, Farfesa Garba Ibrahim Sheka sun ce tattalin arzikin Nijeriya na tafiyar hawainiya bayan hukumar kididdiga ta ce kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta yi fama da shi.
Source: BBC Hausa
Title :
Sai Yan Nigeria Sun Koshi Zan Yarda Tattalin Arziki Ya Farfado-Atiku
Description : Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce akwai sauran rina a kaba kafin hukumomin kasar su tabbatar da an kawo karshe...
Rating :
5