Rahotanni daga birnin Kano a Nigeria na cewa an ji wa mutane da dama rauni ciki har da wasu manyan jami'an tsagin siyasar Kwankwasiyya bayan da 'yan daba suka farma mutane a wurin hawan Daushe.
Wasu da suka shaida lamarin sun fada wa BBC cewa wasu 'yan adaban, wadanda ake zargin magoya bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne, sun farma magoya bayan Tsohon Gwamna Rabi'u Kwankwaso, wadanda suka yi fitar dango da jajayen hulanansu.
Suka kara da cewa yawancin wadanda lamarin ya shafa an yanke su ne da wuka yayin da aka sari wasu da manyan makamai, kamar adda da takofi.
Wani na hannun daman Kwankwaso ya shaida wa BBC cewa an ji wa manyan jami'ansu da suka hada da tsohon Sakaren Gwamnatin Kano Rabi'u Suleiman Bichi ciwo, kuma ya dora alhakin lamarin kan gwamnatin jihar.
Kawo yanzu rundunar 'yan sandan jihar ba ta ce komai game da lamarin. Sai dai gwamnatin Kano ta ce ba ta hannu ko kadan a lamarin da ya faru.
Sai dai Kwamishinan Yada Labarai na Kano Mohammed Garba ya shaida wa BBC cewa bai san da labarin rikicin ba sai bayan an gama hawan, amma ya ce sun samu bayanan cewa "'yan Kankwasiyya sun shirya tayar da hankali a wurin".
Hawan daushe, wanda sarkin Kano ke jagora kwana daya bayan kowacce sallah, na jan hankalin jama'a da dama ciki har da 'yan yawon bude ido.
Hakkin mallakar hotoOTHERImage captionWani da aka sara a wurin hawan na Daushe
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna wasu magoya bayan Kwankwasiyya na karbar magani a asibiti da jini a jikinsu.
"Na ga jama'a da dama suna gudu, wasu kuma a kwance, yayin da wasu 'yan Kwankwasiyya suka rinka boye jajayen hulunansu domin kada a gane su," a cewar wani ganau, wanda ya nemi a boye sunansa.
Da dama daga cikin wadanda suka jikkata na samun kulawa a asibitin koyarwa na Aminu Kano da sauran asibitocin birnin.
Kwamishinan yada labarai Mohammed Garba ya kara da cewa "Mun je wurin, kuma mun dawo lami lafiya, inda jama'a suka yi ta murna suna daga wa Gwamna Ganduje hannu."
Ya kara da cewa dama an saba samun yamutsi a wuirn Hawan Daushe amma dai gwamnati ba ta da hannu a cikin lamarin, kuma ba ta goyon bayan abin da ya faru ko kadan.
Dama dai 'yan siyasa na amfani da hawan na Daushe, wanda ake yi kwana daya bayan sallah, domin nuna karfin magoya bayansu.
Magoya bayan Kwankwasiyya kan yi dandazo da jajayen hulanansu, yayin da su ma magoya bayan Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje ke halatta.
Source: BBC Hausa
Title :
Anyi Sare Sare A Hawan Sallar Kano
Description : Rahotanni daga birnin Kano a Nigeria na cewa an ji wa mutane da dama rauni ciki har da wasu manyan jami'an tsagin siyasar Kwankwasiyya b...
Rating :
5