An dakatar da 'yan kwallo tara daga buga wasa 12, kuma an dakatar da jami'an wasan kwallon kafa biyu daga gudanar da wasa 19, a dalilin kai wa wasu jami'an wasan hari a wasannin Firimiyar Najeriya.
A bara kungiyar da ake tuhuma mai suna FC Ifeanyi Ubah ta zama kawar kungiyar West Ham ta Ingila.
A lokacin wasan a watan Agusta 'yan kwallo uku sun kai wa alkalin wasa Nakura Auwal hari bayan da aka bai wa dan wasan kungiyar, King Osanga jan kati.
Daga baya kuma 'yan wasa shida sun far wa alkalin wasan, kuma Chidi Nwogu da Adrika Obiefuna wadanda suma jami'an kungiyar ne suka ci mutuncin alkalan wasan.
Firimiyar Najeriya ta hukunta biyu daga cikin 'yan wasan, Stephen Eze da Adeleye Olamileka, kuma 'yan wasan biyu sun taba murza wa Najeriya leda a tawagar gasar zakarun kasashen Afirka.
Haka kuma an ci tarar kulob din dala 4,900 a kan abin da ya faru, an kuma umarce su su biya dala 700 ga ko wanne jami'in da abin ya rutsa da shi, da kuma biyan kudin maganinsu.
Source: BBC Hausa
Title :
Ansawa 'Yan Kwallon Nigeria Takunkumi
Description : An dakatar da 'yan kwallo tara daga buga wasa 12, kuma an dakatar da jami'an wasan kwallon kafa biyu daga gudanar da wasa 19, a dali...
Rating :
5