An gabatar da wani korafi na son a kwace lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel daga hannun shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi, saboda yadda sojoji a karkashin gwamnatinta ke kai wa tsirarun Musulmai 'yan kabilar Rohingya hari a yankin Rakhine.
Ta yi watsi da batun cewa kisan kare-dangi a ke yi wa 'yan Rohingya a Myanmar ko Burma, kuma ta ce akwai tashe-tashen hankula daga ko wane bangare.
A nan mun yi waiwaye ne kan rayuwarta ta baya, daga da lokacin da take gwarzuwa mai son kare hakkin dan adam zuwa yanzu da ta zama saniyar-ware a wajen wadanda da suke mara mata baya a duniya.
Source: BBC Hausa
Title :
Anason Kwace Lambar Yabon Shugabar Myanmar
Description : An gabatar da wani korafi na son a kwace lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel daga hannun shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi, saboda yadda so...
Rating :
5