Akalla mutum 100,000 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kananan hukumomi 12 na jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya.
An aike da kayan agaji ga al'ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Benue wadda take tsakiyar Najeriya, kamar yadda hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar (NEMA) ta shaida wa BBC.
A ranar Juma'a ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarci hukumar NEMA da ta aike da kayayyakin agaji ga mutum fiye da 100,000 wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.
Har ila yau shugaban ya jajantawa wadanda al'amarin ya shafa inda ya sha alwashin taimaka musu.
A farkon makon nan ne aka fuskanci mummnunar ambaliyar bayan wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a jihar ranar Asabar da ta gabata
Ambaliyar ta yi sandiyyar raba dubban mutane da muhallansu.
Cikin huraren da ambaliyar ruwar ta shafa har da gidan rediyon jihar da jami'ar jihar da kuma wata babbar kasuwa.
A cikin watan Yuli ne mahukunta a kasar suka yi gargadin cewa kusan jihohi 30 ne za su fuskanci bala`in ambaliyar ruwa a bana, sakamakon mamakon ruwan sama da ake tafkawa.
Source: BBC Hausa
Title :
Ambaliyar Ruwa Ta Tarwatsa Mutum Dubu Dari A Nigeria
Description : Akalla mutum 100,000 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kananan hukumomi 12 na jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya. An aike da kayan...
Rating :
5