Alkalin Babbar Kotun Majistare da ke zama a Umuahia, jihar Abia, ya tura wasu tsagerun kungiyar taratsin kafa Biafra su 60 gidan kurkuku na Aba.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wadanda aka tura kurkukun sun a daga cikin wadanda aka kama sanadiyyar hargitsin da su ka tayar was sojojin Najeriya.
Dukkan su dai ana tuhumar ne su da laifin kona dukiyoyi da kuma kisan kai, kamar yadda PREMIUM TIMES ta ruwaito a baya.
A jiya Lahadi, alkali ya caje su laifin hada baki a aikata barna, kunna wutar fitina, kisa da kuma shiga kungiya ba bisa ka’ida ba.
An iza keyar su kurku sai ranar 25 Ga Oktoba za a zauna kotu.
Source: Premium Hausa
Title :
Alkali Ya Tura Tsagerun Biafara 60 Kurkuku
Description : Alkalin Babbar Kotun Majistare da ke zama a Umuahia, jihar Abia, ya tura wasu tsagerun kungiyar taratsin kafa Biafra su 60 gidan kurkuku na ...
Rating :
5