Shugaban Hukumar kula da cigaban fasahar zamani ta Najeriya wato NITDA, Dr. Isa Ali Pantami ya ce ma fi yawancin ma'aikatan ba su cancanci albashi da suke ci ba.
A wata hira da BBC kan irin aikace-aikace da kalubalen da ma'aikatarsa take fuskanta, Dr. Pantami ya ce "Za ka ga ma'aikata 500 amma bai fi mutum 50 ne suke iya yin aikin da aka dauke su su yi ba."
Ya kara da cewa " Wani idan ka ba shi ya rubuta maka takarda ta minti daya lokacin da za ka dauka wajen gyara rubutun ka kwammace da kanka ka rubuta."