An samu yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya da kasar Amirka wajen siyan jiragen yaki na dalar Amirka miliyan 600 don cigaba da yakar 'yan Boko haram
Rahotanni sun bayyana cewa kasar Amirka ta amince da wata yarjejeniya tsakanin ta da Najeriya wajen sayar da jiragen yaki na kimanin Dalar Amirka miliyan 600 don taimakawa wajen cigaba da yakar 'yan Boko haram.
A ranar Larabar da ta gabata ne ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta bayar da sanarwa ga majalisar dokokin kasar akan shirin gwamnatin kasar na amincewarta wajen sayar da jiragen.
Wannan lamarin ya faru bayan kwanaki 30 na duba kan yarjejeniyar a lokacin da 'yan majalisar kasar ke da damar hana cinikin.
A karshen mulkin tsohon Shugaban kasar Amirka, Barack Obama ne aka dakatar da yarjejeniyar bayan wani jirgin yakin Najeriya ya yi aman wuta kan wani sansanin 'yan gudun hijira bisa kuskure wanda rahotanni su ka bayyana adadin mutum 200 da su ka mutu a wannan tsautsayi.
Wannan yarjejiniya ta bayu ne bayan da shugaban kasar Amirka na yanzu, Donald Trump, ya bayyana ra'ayin sa a kan kara yawan abubuwan da kasar ke sayarwa.
Idan har wannan abu ya tabbata to lallai sojin Najeriya za su dara don daman kullum kukan su rashin kayan aiki ne ya sa ake ta fafatawa da 'yan Boko haram kawowa yanzu.