Hukumar jami'an yan sandan najeriya dake jahar legas tayi nasarar cafke wasu mutune arba'in da biyu da ake zargi da Neman maza(luwadi)
Da yake bayyanawa a gaban manema labarai mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar olarinde famous cole
Yace" jami'an mu sunyi nasarar cafeke wadan da ake zargin ne bayan wani sumame na musaamman da suka kai a wani otel dake Owode-Onirin dake gabashin jahar
legas
Olarinde ya kara da cewa dayawa daga cikin su munada shaidun da ya tabbatar da hakan amma akwai wadan har yanzu babu tabbacin suna aikata wannan aika aika inda suka bayyana mana cewa basu san ana aikata wannan laifi ba agurin ,amma mun tsaresu ne saboda kammala bincike
Wanda da zarar mun kammala bincike zamu gurfanar dasu a gaban kotu da fuskantar hukuncin daya dace dasu
A shekarar Dubu biyu da Sha hudu ne dai tsohon shugaban kasa goodluck Jonathan yasa hannu kan dokar data haramta auren jinsi a najeriya
Inda kuma dokar ta tanadar da daurin shekaru shahudu a gidan yari ga duk wani da aka kama da aikata hakan ko kuma yun kuri aikatawa,
Sai dai haryau tunda aka zartar da dokar ba'a taba hukunta wani da ita ba