Labarin wani matashi da ibtila'in fyade auka masa wanda ya yi shekara da shekaru ya na gudun bayyana abinda ya faru da shi
Wani matashi mai suna Stephen Kigoma dan kasar Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Kongo ya bayyana yadda wa su maza su ka budewa duburarsa wuta.
Stephen ya bayyana labarin yadda faruwar wannan abu ta kasance da shi kuma yana yin kira ga mutanen da suka fuskanci wannan matsala su fito fili su bayyanawa duniya.
Stephen ya bayyanawa manema labarai na BBC cewa " Idan na fadi abin da ya faru, mutane za su guje ni kuma su kansu mutanen da suka yi min magani ba za su sake bani hannu mu gaisa da su ba."
"Na boye cewa an yi min fyade. Ba zan iya fada ba don duk loacin da na tuna abu yana komawa tamkar sabo ne," in ji shi.
"A matsayina na namiji ba zan iya kuka ba domin mutane za su ce ni matsoraci ne, rago, kuma shashasha abin tsokana." An yi min fyade ne lokacin da wasu maza suka kai hari garin mu, Beni da ke arewacin jamhuriyyar Kongo.
"Sun kashe mahaifina. Mutum uku sun yi min fyade, sannan suka ce: 'Kai namiji ne, yaya za ka ce an yi maka fyade? Sun yi hakan ne domin ya zama wani makami da za su yi amfani da shi domin rufe min baki."
Bayan ya tsere daga Uganda a 2011, Stephen ya samu taimakon likitotici inda ya bayyana mu su matsalar sa, bayan an duba an ga cewa babu sauran raunuka a duburarsa.
An kai shi ya ga likitan da ke duba mutanen da aka yi wa fyade a lokutan yaki, kuma shi kadai ne namiji a cikin wadanda likitan ya gani.
"Na ji kamar na nutse cikin kasa don wulakanci. Na je kasar da ba tawa ba domin yi wa likita bayani kan abin da ya faru da ni. Abin da nake jin tsoron da kunyar fada kenan."
Stephen ya samu shawarwari a kan yarda zai manta da abin da ya faru da shi ta hanyar kungiyar debe kewa, wacce ke birnin Kampala na kasar Uganda, inda shi da wasu mutum biyar suka yi bayani kan abin da ya faru su.
Kungiyar debe kewa, wacce ta yi bincike a kan yi wa maza fyade a jamhuriyyar Kongo, ta bayar da rahoto kan yin lalata da 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu a arewacin Uganda su ke fama da ita.
Ta gano cewa fiye da kashi 20 cikin 100 na mata sun kai rahoton yi musu fyade idan aka musalta da maza masu kashi hudu.
Wani likita Dr Chris Dolan ya ce "babban dalilin da ya sa maza kadan ke kai rahoton cin zarafinsu shi ne kada a mayar da su saniyar ware."
Kasar Uganda ta karbi 'yan gudun hijira sosai a 2016 wadanda suka tserewa rikicin Sudan ta kudu. Ya kara da cewa ana fuskantar kalubalen wajen shari'a idan maza suka kai rahoton yi musu fyade.