Limaman majami'u da masallatai a Jihar Kuros Ribas sun gode wa Gwamnan Jihar, Ben Ayade bisa alkawarin da ya yi musu na basu naira miliyan 30, bayan da ya samu nasara a kotun daukaka kararrakin zabe a watanni bakwai da suka gabata, sakamakon addu'o'in da ya sa aka rika yi masa.
A makon jiya ne Gwamnan ya kira shugabannin kungiyoyin addinin Kirista da na Musulunci, inda ya ba su kyautar naira miliyan bakwai domin raba wa daukacin limamai da ke jihar.
Da yake zantawa da manema labarai a Kalaba shugaban kungiyar limamai da alarammomi na Jihar Kuros Ribas Manjo Kabiru Sa’ad Yakubu ya gode wa gwamnan bisa cika alkawarin da ya yi.
“Gaskiya mun yi murna, mun yi farin ciki matuka da gwamnan ya cika mana alkawari ya ba mu Naira milyan bakwai,” in ji Yakubu.
A cewar shugaban limaman: “An ba kowanne limami Naira dubu 100. Kuma hatta sarakunan mu na gargajiya ma an ba su Naira milyan daya da dubu 200, sai abokan aiki na gefe su ma an nema musu wani abu.”
Manjo Sa’ad Yakubu babban limamin barakin soja na Birged ta 13 da ke Kalaba, wanda shi ne shugaban kungiyar ya jawo hankalin ragowar limaman masallatai da suka nuna turjiyar kin shiga kungiyar da cewa ba kungiya ce mai adawa da akida ko ra’ayin addini ba sai don yi wa Musulunci da kuma Musulmi aiki.”
Daga karshe ya bayyana cewa sun ajiye wa sakatariyar kungiyar wani abu, domin ci gaba da gudanar da ayyukanta.
“Maimakon mu rika zuwa bara wurin mutane ya sa muka ware wa sakatariya wani abu,” in ji shi.
Title :
Wani Gwamna Ya Rabawa Limaman Addinai Miliyan 30 Saboda Addu’a
Description : Limaman majami'u da masallatai a Jihar Kuros Ribas sun gode wa Gwamnan Jihar, Ben Ayade bisa alkawarin da ya yi musu na basu naira mili...
Rating :
5