Wannan plate numban motar wani bawan Allah ne da yazo cirar kudi ATM na UBA Bank da ke daura da Fagge Police Station, mutumin wanda bai gaza Shekara 50 ya cire kudin ya koma motar yana waya ashe wayar sa ta karshe
Kenan, ya saka mukuli zai tashi motar Allah ya zare ransa ya amsa kira zuwa gare shi. 'Yan sanda na cigaba da tuntuba don samun 'yan uwan shi.
Allah muke roko yayi masa rahama, wannan mutuwa ta zama Ishara da wa'azantuwa ga duk wanda ya ganta dama wanda yaji labari.