An kama wasu Matasa kwanaki da laifin yi wa wata karamar yarinya fyade. Sai dai wannan Fasto ya shiga ya fita har sai da aka sake masu laifin.
Fasto Johnson Sulaiman ya bayyana haka ne wajen hudubar sa a coci yace an daure wasu mutane har 7 da laifin yi wa wata yarinya fyade sai dai ya bada makudan kudi har Miliyan daya da rabi domin ayi belin su.
Faston yace ya gargadi wadannan mutane da su kayi wannan danyen aiki da su tuba. Ciki dai har da wanda su kayi wa 'Yar shekara 3 fyade. Sauran kuma sun dura kan wata Budurwa ne mai shekaru 16 a Duniya.
Wannan abu dai ya faru ne a Garin Auchi da ke Jihar Edo inda aka daure wadannan mutane tun a Watan Maris. Kwanaki wata Budurwa ta maka wannan Fasto a kotu inda ta ke zargin sa da laifin lalata da fyade da ita da karfin tsiya tare da saba alkawari da kuma mata bata-suna.
Title :
Tir: Wani Limamin coci ya nemawa masu fyade beli
Description : An kama wasu Matasa kwanaki da laifin yi wa wata karamar yarinya fyade. Sai dai wannan Fasto ya shiga ya fita har sai da aka sake masu laifi...
Rating :
5