Kungiyar bayar da agaji ta International Committee of the Red Cross, ta ce har yanzu 'yan gudun hijirar da kungiyar Boko Haram ta fatattaka daga gidajensu a yankin tafkin Chadi na cikin mawuyacin hali.
Kungiyar ta ce ziyarar da ta kai wasu yankuna da bala'in hare-haren boko Haram ya shafa, ta nuna mata cewa akwai sauran rina akaba game da tallafin da ake bai wa 'yan gudun hijirar, tana mai cewa babu abin da miliyoyon 'yan gudun hijirar ke so kamar samun zaman lafiya da komawa gidajensu.
Babban jami'in da ke kula da ayyukan bayar da agaji a yankin tafkin Chadi, Mamadou Sow, wanda ya kwashe kwana goma a arewa maso gabashin Najeriya ya shaidawa BBC cewa,halin da ya tarar da 'yan gudun hijirar na da matukar muni idan akayi la'akari da cewa mutum miliyan biyar daga jihohin Adamawa da Borno da Yobe na matukar bukatar abinci.
Ya ce miliyan biyu daga cikinsu sun bar gidajensu ba su da damar komawa, ba su kuma da damar yin noma da kiwo da kuma kamun kifi.
Mamadou Sow, ya ce ba bu wanda wannan matsala ta fi shafa a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ma yankin tafkin Chadi kamar mata da kananan yara, domin zaka ga mace mai shayarwa ko mai ciki amma ta na fama da tamowa, haka yara ma.
A saboda haka yakamata a kara akan taimakon da ake ba su musamman a irin yanayin da ake ciki na damuna.
Jami'in ya ce, duk 'yan gudun hijirar na samun taimako daga kungiyoyi da dama, dole gwamnatin Najeriya ma ta rubanya abinda ake ba su, bisa la'akari da cewa suma ba a san ransu suka kasance a wannan yanayi ba.
Allah ya sauwaka
Source: BBC Hausa
Title :
Tamowa Ta Fara Kama Yan Gudun Hijira-ICRC
Description : Kungiyar bayar da agaji ta International Committee of the Red Cross, ta ce har yanzu 'yan gudun hijirar da kungiyar Boko Haram ta fatatt...
Rating :
5