A wannan shekarar ne a ka samu dalibin makarantar Farfesa Ango Abdullahi da ke Zariya a jihar Kaduna, Salim Abdulkareem, mai shekaru 6 da ya haddace Alkur'ani mai girma.
Abdulkareem ya kammala haddar ta Alkur'ani mai girma cikin lokacin da bai kai shekara guda ba don ya fara karatun ne a watan Mayun shekarar 2016 kuma ya kammala kafin watan Mayun shekarar 2017.
A yayin tattaunawa da manema labarai, Salim ya bayyana cewa ba shi da wani buri wanda ya wuce ya zamto likita saboda hakan zai ba shi damar taimakawa marasa lafiya kuma ya bayar da gudunmawa wajen samar da al'umma cikin yalwar lafiya.
Daya daga cikin malam makarantar kwanan ta koyon karatun Alkur'ani, Mallam Hamza Jibril wanda ya tabbatar da ingancin haddar Salim, ya ce babban abin alfaharin wannan al'amari shi ne lokacin da aka kawo Salim makarantar ko harufan larabcin bai sani ba.
Baban Salim, Farfesa Abdulkareem S. Ahmed wanda malamin koyarwa ne a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya, wanda ya kawo shi a watan Mayun shekarar 2016 ya dankawa malaman makarantar amanar dan shi, kuma wani lokacin ko hutu a ka yi sai ya ce Salim ya zauna a makaranta ya cigaba da tilawa.
Mallam Hamza ya ce "wannan shi ne sanadiyar da yasa Salim ya yi fice cikin dalibai kuma wannan shine karo na hudu ko biyar kenan da mu ka samu dalibai ma su hazaka kamar Salim.
Ya ce duk lokacin da muka tura daliban mu musabaka su na yin fintinkau a kasar nan da kasashen waje don ko a shekarar da ta gabata wani dalibin mu, Aliyu Shamsuddeen, wanda a lokaci shekarun shi 3, ya yi na biyu a gasar karatun Alkur'ani ta duniya da aka gudanar a kasar Saudiya.