A daren ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin jihar Benuwe tare da hadin gwiwar 'yan sandan jihar suka kai simame gidajen karuwai 5 wanda su ka cafke kimanin guda 72 a birnin Makurdi.
Wannan kamen na karuwai ya fayu ne sanadiyar da wata kungiyar mata su ka nuna kukan su da yin zanga-zanga a kan yadda yiwa kananan yara fyade da lalata su yake karuwa a jihar.
Shugaban mai baiwa gwamntin jihar shawara a kan harkokin tsaro, Col, Edwin Jando ya bayyanawa wannan kungiyar ta mata cewa gwamnatin gwamna Samuel Ortom ba za ta lamunci wannan gurbatanci da yake faruwa a jihar ba.
Jando ya ce yunkurin da gwamnatin jihar ta ke wajen kawar da faruwar fitintinu a jihar ne ya sa suka cafke wannan karuwai a gidajen sana'ar su.
Title :
Photos: An Kama Masu sana'ar karuwanci 72 a jihar Benuwe
Description : A daren ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin jihar Benuwe tare da hadin gwiwar 'yan sandan jihar suka kai simame gidajen karuwai ...
Rating :
5