Shugaban majalisar tarayyar Najeriya Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa majalisar ta tarayya ta shirya tsaf domin yi wuwar yin kwaskwarima ga tsarin mulkin Najeriya wajen karin mafi karancin albashi.
Sanata Saraki yayi wannan ikirarin ne a garin Abuja yayin da yake fira da manema labarai inda ya bayyana cewa tabbas majalisar ta san halin da talakan kasar nan yake ciki kuma za su duba suka yadda zasu taimaka masa.
kuma yace dukkan alkaluman da suka sa aka saka N18,000 a matsayin mafi karancin albashi yanzu sun canza don haka done ne shima albashin ya canza.
Daga karshe Sanatan sai ya bayyana cewa su a shirye suke da zaran fadar shugaban kasa ta basu umurni su gaggauta bi don inganta rayuwar talaka.