Hukumar 'yan sandan Najeriya ta kaddamar da wani cikakken bincike a kan satan da aka yi a gidan tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan a babban birnin tarayya, Abuja.
Sanarwa hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewa bincike na farko ta nuna cewa wasu abubuwa ne kawai barayin suka yi awon gaba da su daga gidan.