Ranar juma’a tana da wani lokaci na musamman da Allah yake amsar addu’o’in
bayinsa a cikinsa. Annabi s.a.w ya bayyana haka:
1-Annabi s.a.w ya ambaci ranar juma’a sai
ya ce:
(a cikinta akwai wani lokaci da babu wani bawa musulmi da zai dace shi,yana Sallah
yana rokon Allah acikinsa wani abu, face Allah ya basa). “Qudaibata ya kara acikin riwayarsa, sai Annabi s.a.w yayi nuni da Hannunsa yana nuna lokacin kadanne”
@Bukhari da Muslim da Malik a Muwaddha da Ahmad.
2-Manzon Allah s.a.w yana cewa: (Lallai aranar Juma’a akwai wani lokaci wanda babu wani musulmi wanda zai dace da wannan lokacin yana tsaye yana Sallah yana rokon Allah wani alkhairi face sai Allah ya basa). Sai ya nuna da hannunsa lokacine
kadan.
@Bukhari da Muslim da Nisa’I da Ibn Majah da Ahmad.
3-Annabi s.a.w ya ce:
(Lallai aranar juma’a akwai wani lokaci, wanda babu wani bawa musulmi zai dace
dashi yana rokon Allah alkhairi acikinsa,face sai Allah yabashi abin da ya roko) kuma lokacine kadan.
@Muslim Malamai sun yi sabani akan wani Lokaci ne wannan:
Ibn Qayyim R.A yana cewa:
“Malamai sunyi sabani akan wannan lokacin na ranar juma’a,an sami maganganu guda
goma”.
@Zadul Ma’ad.
Amma maganar da tafi karfi acikin gomar magance guda biyu:
1-Daga hawan Liman kan Mumbari zuwa kare Sallah.
Dalili akan wannan shi ne:
“Abinda Imam Muslim ya ruwaito acikin Littafinsa daga Hadisin Abi Buraidah bn Abi
Musa:Lallai Abdillahi dan Umar R.A ya ce da shi:
Shin kaji babanka yana bada Hadisi daga Annabi s.a.w akan Lokacin Amsa addua a ranar juma’a??? Sai ya ce EH: Na ji shi yana cewa: naji Annabi s.a.w yana cewa:
(Shine tsakanin Zaman Liman akan Minbari zuwa kare Sallar juma’a).
@Mulim.
Kuma Ibn Majah ya riwaito a cikin Sunan nasa daga Amru ibn auf R.A ya ce: An tambaye Annabi s.a.w game dA lokacin amsar addua a ranar juma’a sai ya ce: (Daga tada Sallah zuwa gama Sallar juma’a).
@Ibn Majah da Tirmizy
2-Bayan Sallar La’asar: Kuma Malamai sukace wannan magana itace
mafi rinjayen magana. Ita ce maganar Abi Huraira R.A da Abdillahi Bn Sallam R.A da Imam Ahmad da sauran Malami da dama. Hujjarsu ita ce:
Daga Abi Sa’I’d da Abi Hurairata R.A suna cewa: Lallai Annabi s.a.w yace: (Lallai a ranar juma’a akwai wani lokacin da babu wani bawa musulmi wanda zai dace da wannan lokacin yana rokon Allah alkhairi a cikinsa face sai Allah ya bashi,shine bayan Sallar La’asar).
@Ahmad
A hadisin Jabir bn Abdiilah R.A Annabi s.a.w yace:
(……….Ku nemi wannan lokacin a sa’ar karshe bayan SallaR La’asar).
@Abu Dauda da Nisa’I.
Allah ne mafi sani.