A kokarin da jam'iyyar APC ke yi na tabbatar wa da talakawa cewa tayi wata babbar hobbasa tun bayan da suka zabota, shugaban jam'iyyar yace zuwansu ne kadai ya ceci Najeriya.
A cewarsa dai, da ba'a zabi shugaba Muhammu Buhari a 2015 ba, to da lallai kasar nan tuni ta kai ga wargajewa, domin wai a cewarsa, irin barnar da aka tafka a baya, dama rashin alkiblar waccan gwamnati
John Oyegun na wadannan furuci ne a lokacin da yake karbar 'yan siyasar jihar Delta wadanda suka tsere daga jam'iyyarsu ta PDP.