AN SOKE ZABEN TSOHON DAN MAJALISSAR DATTAWA DAVID MARK
.
Daga M. Kabiru Muhammad
.
Kotun daukaka kara dake garin Makurdi ta soke zaben tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark.
.
Kotun ta umurci hukumar Zabe da ta sake Zabe a yankin nan da kwana 90.
.
Dan takaran kujeran sanata na jam'iyyar APC Donald Onjeh ne ya kai karan rashin amincewa da sakamakon zaben tun a wancan lokacin.
.
Mai sauraron sharia'ar ya nemi hukumar INEC da ta gudanar da sabon zabe a yankunan nan da watanni uku.
.
Yayin da wasu Al'ummar Jihar suke Allah wadai da wannan Hukunci.
.
Wasu kuma Sun Yabawa Kotun da cewar"Hakan da akayi shi ne Dai-Dai".
.
Shin Ko Sauran Al'ummar Nigeria sun Gamsu da Wannan Hukuncin?
Title :
AN SOKE ZABEN TSOHON DAN MAJALISSAR DATTAWA DAVID MARK
Description : AN SOKE ZABEN TSOHON DAN MAJALISSAR DATTAWA DAVID MARK . Daga M. Kabiru Muhammad . Kotun daukaka kara dake garin Makurdi ta soke zaben t...
Rating :
5