Alhamdulillah Mai Girma Sanatan Bauchi ta arewa Engr. Dr. Suleiman Nazif yayi nasarar samowa asibitin shaka tafi akowani local government dake katagum zone, wanda za'agina a dukkanin chikin kwaryar kowani karamar hukuma.
Wannan asibitin za'ana bada magani kyauta ga dukkanin mata masu chiki dakuma kananan yara yan kasa da shekara biyar, a duk lokacin da bukatar hakan yataso, yanzu haka ansamu dukkanin filayen da za'agina wadannan asibitotin a dukkanin kananan hukumomi guda bakwai damuke dasu.
Na garin GAMAWA harma anyi rufi yanzu haka, Garin JAMA'ARE ansamu fili haka ZAKI, SHIRA, GIADE, ITAS dakuma AZARE wanda yan Unguwane suka bada kyautar Fili a Opposite State lowcost Azare don Gina wannan asibitin.
Alhamdulillah wannan dama shine Babban abinda muke bukata ana kawo mana don anfanan Talakawa marasa karfi dama sauran al'ummah baki daya, Allah ubangiji yakara muku karfin gwiwwa wajen kawowa alkhairi a jama'a.
Source from aminiya