Wasu abubuwan fashewa da dama sun tashi a birnin Maiduguri da kuma cikin Jami'ar Maiduguri a jiya Asabar.
Da yake magana a kan batun kakakin Jami'ar Maiduguri Farfesa Danjuma Gambo ya tabbatar da lamarin a cikin Jami'ar, ya kuma shaidawa manema labarai cewa an samu asarar rayuka na Jami'ar tsaro a Jami'ar da kuma jikkatar wasu mutum biyu.Bamabaman dai sun tashi a wurare uku ne a cikin Jami'ar.
A kwai Wanda ya tashi a ofishin Jami'an tsaro da kuma wadanda suka tashi gabar da Jami'ar sakamakon rashin Katanga ta bangaren.
Yanzu haka an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti don yi musu magani.