Daga Mahmud Isa Yola
Mu muna nan ne a Arewa ba a jihar Osun ba. Amma labarin da yazo mana shine: wani dan Arewa matashi ya mari matar wani Taana (kuyi hakuri na kira shi da sunan Taana saboda shine ƙurewa a kasanci) a bakin shagon ta. Daga nan ita kuma ta kira mijin ta Tana ta sanar dashi abunda ke faruwa shi kuma ya gayyato ‘yan uwan shi, suka kashe iya abunda zasu iya kashewa cikin mutane sannan kuma suka wawuri dukiyan jama’a iya son ran su.
A cikin wannan labari akwai abubuwa guda biyu ma banbanta.
Idan da labarin ya kasance cewa wani bahaushe ya mari matar wani bayarbe ne, sai bayarben ya zo don ramuwa, kuma ya rama mata, ko kuma ya gayyato mutanen shi suka rama wa matar kan Bahaushen da yayi marin, to wannan ba sabon abu bane kuma a matsayin shi na namji yana da hakki yabi kadun matar shi.
Amma abun ya kai ga kisan mutane wadanda basu ji ba basu gani ba har sama da mutum ashirin, wannan wani babban abu ne na daban.
Ina nufin zarcewa da suka yi har suka kashe mutane sama da ashirin, ba yana nuna wa cewa ramuwar gayya suke yi ba. Abun da wannan yake nuna wa shine dama suna cike da wadannan Hausawa dake zaune tare da su. Sun jima suna neman sanadi amma sai yanzu suka samu, wannan yasa rikicin da ya shiga tsakanin Bahaushen nan da bayarbiya nake ganin shi abu na daban. Haka kuma kisan gilla da aka yi wa Hausawa mazauna garin Sabo, cikin Ile Ife shima nake ganin shi a matsayin abu na daban.
Shi rikicin dake tsakanin matashin nan da bayarbiya rikici ne da ko yaushe ana iya samun shi tsakanin mutane biyu ko fiye, wannan yasa zakaga hatta harshe ma da hakori sukan yi sabani. Kuma ita matar idan har ya mare ta, tana da dama cikakke da zata nemi mijin ta don ita ba namji bace da zata fiskance shi.
Amma kisan gillan nan, wannan wani mummunan makarkashiya ce da dama an dade ana shirya shi, an jima ana tsumayin ranan da za’a aikata hakan akan wannan mutane, yanzu kawai an samu sanadi ne abun ya bayyana.
Sun far wa Hausawan nan ne da niyyan kassara su na har abada, sun kona musu shaguna. sun kwashe musu dimbin dukiyoyin su, sun musu kisan wulakanci tamkar dabbobi, wasu sun sassare su, wasu sun harbe su, wasu sun kona su da ran su!
Yarbawa mazauna garin Ile Ife sun tabbatar mana da cewa duk abunda dabba zai aikata, to mutum zai iya aikata abunda ya fi shi.
Ba rayukan Hausawan nan ne kadai suka hara ba, sun hari dukiyoyin su. Da dama na karanta labaru cewa sun rasa miliyoyi kudi, wannan wadanda suka tsira da rayukan su muke magana.
Alamu sun nuna cewa wadanda suka aikata wannan aika aika sun aikata hakan ne a bisa dalili daya. Wannan dalili kuwa ba zai wuce kyashi da suke dashi akan habakar kasuwancin bakin su Hausawa ba.
Garin na Ile Ife kuma gari ne da yake da Hausawa fiye da kowani yanki a jihar Osun. Hausawa sun dade a wannan wuri, wasu ma na hasashen cewa garin Sabo gari ne da asali yake mallakan Hausawa.
Babu shakka gwamnati ta dauki matakai da suka dace kawo yanzu, to amma wannan matsala ba ta gwamnati kadai bace, matsala ce da nake gani Sarakunan gargajiyan wannan yanki ya kamata su warware.
Kaman yanda na sha fada a rubutu na cewa, mutane sun fi kusa da wadannan shuwagabanni fiye da gwamnati, kuma su din sune shuwagabannin abun da ake fada akai, wato kabilu. Wannan yasa nake gani sune ya kamata su fara kiran al’umman su su gargade su akan illan abunda suke aikatawa.
Akwai ‘yan uwan su a Arewa, yau da gobe ba abun da ya bari. Hakan da suke yi suna jefa rayuwar ‘yan uwan nasu ne cikin hatsari. Haka kuma fa idan sun manta ya kamata su tuna, Hausawan nan da suka yi wa kisan wulakanci fa ‘yan kasuwa ne da suke sayar da kayan masarufi da ba’a noma su a kudu. Idan har suka kashe su, to ina makomar masu bukatan kayakin su?
Naga wani hoton gawar wani an kashe shi a wurin sana’an shi, gawan shi na kwance akan Albasa da yake sayarwa. Abunda na fara tunawa da naga wannan shine tunda sun kashe shi, wa zai kawo musu Albasa kuma?
Yanzu haka da dama Hausawa mazauna garin, wadanda sun riga sun yi jijiya a garin suna dawowa Arewa. Wannan babban koma baya zai jawo wa ‘yan garin saboda zasu dau shekaru masu dimbin yawa suna ji ajikin su ta fannin kasuwanci.
Kisan gilla wa wata kabila ko wace iri ce ba karamin illa bane ga cigaban kasa. Yin hakan da farko zai kara sanya gaba ne cikin zukatan wadanda abun ya shafa, sannan kuma zai kara janyo wata baraka a kasa. Kuma rikicin idan an fara shi zai rika tafiya ne ba iyaka. Wanda aka ci gaplaba akan ta zata koma shirya wa don ramuwa.
Al’umman kasar Nijeriya ya kamata su gane cewa, zaman lafiya shine ginshikin cigaban kasa, idan har babu zaman lafiya to kasa babu yanda zata cigaba. Idan kuma kasa bata cigaba ba, to al’umman cikin kasar suna cikin tashin hankali a koda yaushe.
Za’a iya samun marubuci a:
08106792663 (Text)
isamahmud77@gmail.com
Facebook: www.facebook.com/mahmud.isa.752