A karo na biyu cikin kwanaki biyar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban majalisan dattijai, Bukola Saraki a gidan Abuja dake birnin Landan, inda shugaban kasan yake hutu.
Labarin ganawar ta shugabannin biyu ya fito ne ta kafar yada labarai na shugaban kasa ta twitter @NGRPresident.
"A yammacin yau, Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ganawa da Sanata Saraki a gidan Abuja" inji shafin twitter na shugabab kasa.
Wani makusancin Bukola Saraki ya shaida wa majiyar mu ta Leadership cewa uban gidan sa Saraki ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Landan da yammacin jiya.
Amma sai sai dai ba'a bayyana dalilan sake zaman na shuwagabbin ba.
Ganawar ta su a jiya yana zuwa ne bayan kwanaki biyar da shugaban majalisan dattijai, Bukola Saraki ya jagoranci shuwagabannin majalisan tarayya, tare da kakakin majalisa Yakubu Dogara saboda ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Shuagaban majalisan dattijai a cikin wani bayani da ya fitar ranan laraba da suka gana da shugaban kasa, yace shi da tawagar shi sun ji dadi saboda yanda suka samu shugaban kasan yana lafiya cikin walwala da jin dadi.
Title :
Buhari Ya Sake Ganawa Da Saraki A Landan
Description : A karo na biyu cikin kwanaki biyar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban majalisan dattijai, Bukola Saraki a gidan Abuja dake...
Rating :
5