Masarautar Kano tare da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki a jahar na yunkurin fito da wani shiri na hana auren wuri da zummar inganta lafiyar ma’aurata da kuma rage kamuwa da cutar yoyon fitsari.
Mai martaba sarkin Kano Mallam Muhammad Sanusi na II shi ya bayyana haka yayin da yake jawabinsa a wani taron inganta lafiyar mata da yara a jahar Kano.
Sarkin ya bayyana cewa dole ne mahukunta su yi duba akan kalubalen da mata matasa ke fuskanta a Nijeriya musamman ma a Arewacin Nijeriya, inda alkaluma ke nuna cewa matsalar ta fi baci.
Ya ce ana samun yawaitar rasuwar mata da jinjirayensu a Arewa a sakamakon aure da ake yi wa yara kanana, kuma alkaluma sun nuna cewa arewacin Nijeriya ta fi samun wannan matsala, kamar yadda ta fi fama da matsalar talauci.
A fadarsa, mai yasa kasashen musulunci kamar su Moroccco, Malaysia, da Egypt ba su samun wadannan matsaloli duk da cewa su na gudanar da rayuwar su ne a bisa koyarwar addinin mususlunci?
Shi ma daraktan hukumar kula da lafiyar iyali na majalisar dinkin duniya, UNFPA Farfesa Babatunde Osotimehin, ya bayyana cewa rashin ilimin ‘yaya mata shi ne mafi girma a cikin dalilan da ke haifar da mace macen kananan yara da kamuwa da cututtuka a yankin Arewacin Nijeriya.
Ya kara da cewa bincike a nuna cewa akwai alaka mai karfi tsakanin ilimin uwa da kuma halayen kula da lafiyar ta da na iyalanta.
Ya ce dole ne a tabbatar da cewa yara mata sun tsaya a makaranta sun kammala karatunsu, ba ta re da la’akari da ko sun fito daga birane ko kauyuka ba.
Ya ce wannan ya na da matukar muhimmanci ga lafiyarsu da ci gabansu da ta iyalansu da ta al’umarsu da ma kasa baki daya.
Sarkin Kano ya bayyana cewa an riga an kafa kwamiti kuma ta na samun hadin kan gwamnatin Kano domin ta kafa dokan akan wannan al’amari.
Ya kuma yi kira da ‘yan sandan jahar da su tabbatar da cewa idan an kafa dokar, an bita yadda ya kamata.
daga alummata.com