Inna Lillahi Wa'inna Ilahi Raji'un
Hadarin mota ya yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane biyu a daidai garin Dakatsalle dake jihar Kano bayan sun baro wurin wa'azin kasa da kungiyar Izala ta gudanar a jihar Kano, inda suke kan hanyar su ta zuwa garin Makarfi dake jihar Kaduna.
Muna addu'a Allah ya jikansu wadanda suka ji rauni kuma Allah ya ba su lafiya.