Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje yayi barazanar bincikar gwamnatin wanda ya gada Rabi’u Kwankwaso.
A wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai, matasa da al’adu, Alhaji Muhammad Garba ya sama hannu ya kira barazanar kai gwamna Ganduje Kara idan bai bar sa jar hula ba cikin awowi 48 a matsayin rashin sanjn ciwon kai daga ‘yan barandan siyssa da basu san ciwon kansu ba. Ganduje, ya kuma ce yadda ake murde gaskiya da kuma karerayin da ake yadawa na iya tunzura gwamnatinsa yin fito- na- fito.
Governor Ganduje da Senator Kwankwaso

KU KARANTA: Jihar Sakkwato zata hada hannu da hukumar Soja don kafa makarantu
Ga abinda sanarwar ke cewa: “Hankalin gwamnatin jihar Kano ya karkato kan zargi maras kan gado na sakarci da akeyi na kai karar gwamnati da kuma mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda wasu manyan mabiya akidar Kwankwasiyya suka yi ranar Juma’ar da ta wuce.
“Wannan dabi’a mai ban takaici, maras kunya wadda ba tayi dai dai da siyasar mutunci ba wadda kuma alamu ne na manyan masu akidar Kwankwasiyya abin dariya ne da tausayi na kokarin yaudarar jama’a domin bata gwamnati da gwamna Abdullahi Umar Ganduje.”