Gidan rediyon BBC Hausa ya bayyana Aisha Muhammad Sabitu a matsayin wacce ta lashe gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai.
Aisha, wacce ta fito daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, ta rubuta kagaggen labarinta ne mai suna "Sansanin 'Yan Gudun Hijira".
Labarin nata ya yi tsokaci ne kan mawuyacin halin da 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu suka samu kansu a wani sansani da ke jihar Adamawa.
An zabi labarin ne bayan fafatawar da matan da suka shiga gasar suka yi, kana alkalai kan gasar suka tantance labarai uku da suka dace da ka'idojin da aka shimfida.
Ta shaida wa BBC cewa "Ban taba zaton suna na zai fito ba, ballantana ma a ce ni na zo ta daya. Na yi kuka saboda murna domin ban taba zato ba".
Amina Hassan Abdulsalam ita ce ta zo ta biyu a gasar, inda ta rubuta labari mai suna "Sai Yaushe?", yayin da Amina Gambo ta zo ta uku da labarinta mai taken "In Da Rai".
Daya daga cikin alkalan gasar, Dr Aliya Adamu Ahmad ta ce lokacin da aka gayyace ta domin zama daya daga cikin alkalai ba a gaya mata sunayen sauran alkalan ba.
"Amma mun yi ittifaki cewa labarin da ya zo na daya shi ne kusan dukkanmu muka amince da shi. Hakan ya nuna irin yadda aka gina labarin da tsara shi da kuma salon harshen da aka yi amfani da shi".
Wannan ne karo na farko da Sashen Hausa na BBC ya sanya gasar kagaggaun labarai ta mata zalla.
Editan riko na BBC Hausa, Jimeh Saleh, ya ce: "mun gamsu da irin yadda aka nuna sha'awar shiga gasar da kuma irin labaran da aka turo, muna kuma farin ciki ganin cewa mun bai wa mata damar fadar labaransu."
A ranar Juma'a ne za a bai wa matar da ta lashe gasar lambar yabo, yayin da su ma wadanda suka zo matsayi na biyu da na uku za su samu na su kyaututtukan a wajen bikin da za a yi a Abuja, babban birnin Najeriya.
Madogara BBC Hausa
Title :
Aisha Muhammad Sabitu Ce Ta Lashe Gasar Hikayata Ta BBC Hausa
Description : Gidan rediyon BBC Hausa ya bayyana Aisha Muhammad Sabitu a matsayin wacce ta lashe gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai. Ais...
Rating :
5