. Ba ƙaramin tsoro taji ba a lokacin da ta haɗa
ido da Anty, haka dai ta sauke kanta ta cigaba
da cin abinci. A karo na biyu, Dad ya kore shirun
da ya ziyarcesu ta hanyar cewa "Mus'ab zaran
Yayanka ya dawo, ka shirya tafiya Netherlands
dan cigaba da karatunka na Engineering." hakan
yasa duk suka ɗago kai suka kalli Mus'ab
bakinsa a washe yace "oh Dad! Netherlands basu
kai USA masana Engineering ba, da kawai can
ka kaini." Mom tace dashi "to mene
bambancinsu? Ba duk ƙasashen turai bane?" ƙala
Anty bata ce ba, hasalima ko kallonsu bata yi.
Mus'ab yana wani lauɗi da wuya yace "Moma,
turai ne. Amma ko turan suna suka tara ai.." jin
Mus'ab ya dage akan lallai USA yake so, yasa
Dad yace "shikenan, duk lokacin da kaje Abuja
ka nemi visa da kanka." da haka Alh. ya miƙe ya
bar teburin, Haj. Itama ta bi bayanshi suka shiga
ɗaki... Mus'ab shima ya shige ɗakinsa, Anty ta
kwashi jiki itama zuwa nata ɗakin. Ganin kowa
ya watse an bar Zareenah ita kaɗai ga kuma
dare yayi, yasa ta ɗaga murya ta kira Amina
suka fara harhaɗa kayan abincin zuwa kicin.
"wallahi koh? Ji nake kamar na kori yau, gobe
tazo yanzunnan." cewar Zareenah dake kan
kitchen cabinet tana fuskantar Amina wacce
aikinta na wanke-wanke ta saka a gaba, ko
kallonta bata yi ba tace "hmmm.. Me kike ci na
baka na zuba? Awa nawa ya rage goben tayi?"
haka suka cigaba da hira Amina tana wanke
kayan abincin har ta gama sannan kowacce ta
nufi ɗakinta. . Washe gari da safe bayan an
kammala karin kumallo Dad ya kira Mus'ab a
falo tare da sauran ƴ'an gidan "nayi magana da
Khalid yace tashar Abuja ya sauka, kaga kawai
kaje Abujan ka ɗaukoshi, daga nan kayi batun
Visa. Ko ya kace?" jawabin Alh. Kenan da ya
ƙareta yana kallon Mus'ab da alamar tambaya,
kai ya gyaɗa ya bashi amsa "haka za'ayi, yanzu
zan shiga in shirya sai na tafi." Zareenah tana
gefen Haj. Tace "zaka je dani Bros?" Haj. Ta riƙe
hannunta tace "babu inda zakije, ki bari yaje ya
kawo miki yayan naki mana!" Mus'ab ya shiga
ciki ya shirya sannan ya fito da key na motarshi,
ya sallamesu ya kama hanya.. - *ABUJA CITY* -
Bayan doguwar tafiya da Mus'ab yayi, sai gashi
a gaban wani makeken Hotel wanda sunansa
yake maƙale a can sama kamar haka
"TRANSCORP HILTON" kaitsaye ciki ya shige da
wayarsa kare a kunnansa. Daidai ma'adanin
motocin na Hotel ɗin Mus'ab ya kira Khalid
"kana ina?" muryar Khalid kenan da ta ziyarci
kunnensa, yana fitowa daga motar yace "ina
gurin parking, yi sauri ka fito akwai inda
zamuje!" jin haka yasa Khalid wanda ke tsaye
cikin ɗakin da ya kama yace "ina zamuje?" "oh
Bros! Kadai ka fito!" ya faɗi yana yarfi da hannu,
jin yadda Mus'ab yake magana yasa Khalid ya
fahimci da akwai muhimmin abu da ya kawoshi
Abuja bayan zuwa ɗaukarshi, da wannan tunanin
ya ajiye waya ya ɗau jakar kwamfiyutarsa da na
kayansa ya fito.. Nan Mus'ab ya karɓi kayan ya
watsa a bayan mota "kai malam! Laptop ɗina
yana ciki." Khalid ya faɗi haka yana fara'a ganin
yadda ƙanen nasa ya damu su bar Hotel ɗin,
bayan motar ya buɗe ya ɗauko kwamfiyutar
sannan suka kama hanya. Kaitsaye tashar jirgin
saman da Khalid ya sauka, can yaga sun koma.
"wai me zamu yi nan?" ya tambayeshi, sai a
lokacin Mus'ab ya sanar dashi abinda ya
kawosu. Suka shiga, basu fi mintuna 20 ba suka
kammala komi suka fito zuwa cikin mota. A
lokacin yamma tayi sosai, amma haka ya ja
mota suka kama hanyar komawa Kaduna.
Lokacin Magrib ta riskesu a hanya, haka suka
tsaya su biyu suka sallaceta sannan Khalid ya
karɓi tuƙi suka cigaba da tafiya.. . Ba su suka
isa ba sai cikin dare, a gidan Hajiya tare da
Amina da Auta (Zareenah) sune suka haɗa liyafa
na musamman dan tarbon Khalid. Ai kuwa da jin
ƙarar mota, Zareenah ta fito a guje. "wa nake
gani haka???" Khalid ya furta haka da sigar
wasa, Mus'ab ya fito daga cikin motar a daidai
lokacin da ta isa gaban Yayanta har ta kasa rufe
baki, yace "to ga yayan naki nan, ki dafa shi
kici." Khalid yace "to idan ta dafani sai me? Mu
shiga ciki kinji." ya riƙe hannunta suka shige. A
tsaitsaye ya tadda iyayensa da Anty da kuma
Amina, kowanne daga cikinsu dariya yake. Gaban
Alh. Ya isa ya rungumeshi "welcome back my
son, I'm proud of you!" Alhaji ya faɗi haka bayan
da ya sakeshi daga jikinsa, Hajiya tana dariya
tace "Sannu da zuwa yarona." Anty da Amina
suka ce "Barka da zuwa." murmushi bai ɗauke
daga fuskarsa ba, ya amsa musu gami da maida
kallonsa ga Zareenah yace "me kike ci haka??
Naga you look taller than yadda na barki." tace
"ka tambayi Amina!" sukayi dariya tare sannan
Amina tace "ka shiga ciki kayo wanka, sannan
kazo kaga abinda takeci."
Title :
Zareenah Part 2
Description : . Ba ƙaramin tsoro taji ba a lokacin da ta haɗa ido da Anty, haka dai ta sauke kanta ta cigaba da cin abinci. A karo na biyu, Dad ya kore ...
Rating :
5