A wani mataki na tsuke aljihun gwamnati sakamakon karyewar tattalin arzikin Nijeriya, Fadar Shugaban kasa ta kafa wani kwamiti wanda zai duba yadda za a rage yawan jiragen sama da Fadar Shugaban kasa ke amfani da su.
Rahotanni sun nuna cewa a halin yanzu akwai jiragen sama kusan 10 a Fadar Shugaban kasa ba ya ga kananan jirage masu saukar Angulu. Ana dai sa ran za a rage jiragen daga 10 zuwa 3 bisa umarnin Shugaban kasa. Ana dai ci gaba da guna guni kan irin kudaden da ake narkawa wajen kula da jiragen inda wani rahoto ya nuna cewa an kashe sama da Naira Bilyan biyar a tsakanin watanni 15 wajen sayen man da jiragen ke amfani da shi.
Title :
Za A Rage Yawan Jiragen Shugaban Kasa
Description : A wani mataki na tsuke aljihun gwamnati sakamakon karyewar tattalin arzikin Nijeriya, Fadar Shugaban kasa ta kafa wani kwamiti wanda zai du...
Rating :
5