Daga Hamisu Hassan Ahmed
A kasar hausa duk inda kaji ance
'Yar Talla to ana nufin wata mace
wacce take dauko kayan siyarwa
take yawo kwararo-kwararo
tana tallan kayanta, wata kuma
takan dauki kayan tallanta taje
xuwa kasuwa ko kasuwanni
takasa kayanta, amma a irin
wannan 6angaren na kasuwanni
tallan yafi karkata ga kayan
abinci, ruwa, ko kuma lemo da
kayan zaqi, amma mafi shaharan
kayan tallan mata sune tallan
GORO, KAYAN MIYA, da
sauransu.......
Mutane da yawa sun kasa gane
illar tallar 'ya mace, yayinda wasu
kuma sun sani amma sun take
saboda irin ribar da ake samu a
cikin harkar, wata tana amfani da
'yarta wajen samun kudi, wasu
sakamakon talauci ko kuma
maraici, zakaga yarinya budurwa,
katuwa, baliga amma tana yawo
lungu da saqo da faranti akanta
tana tallan GORO, wanda bazai
wuce na 1500 ba, ko kuma inda
ake gine-gine domin masu
yawan shekaru ko masu shan
taba-sigari sunfi tu'ammali da
GORO, idan akayi rashin sa'a a
irin haka wasu lalatattun matasa
kanyi amfani da wannan damar
wajen bawa yarinya duka kudin
goron ita kuma suyi lalata da ita,
bafa wai lokaci daya zasu bata
kudin ba, a'ah sai sun fara da
yaudararta idan suka sayi na
naira 20 sai su bata 500 idan
tabasu canji sai suce a'ah ta riqe
sun bar mata canjin, wannan zai
sanyaya zuciyar yarinya taga
kamar ko tayi kasuwa ne, idan
'yar kirkice In taje gida sai ta
fada, sai kaji uwarta nafadin a'ah
gobema ki kai masa wataqila
sonki yake saboda tausayinki
dayake, shikenan kuma an bude
mata kofar zuwa gurinsa
ahankali yana yaudararta kuma
shikenan zai furta mata
buqatarta itakuma saboda sanin
zaqin kudi bazata iya bijerewa
buqatarsa ba, shikenan daganan
yasamu damar lalata rayuwarta,
idan kuwa ya fuskanci me sakin
jikice sai yace takai masa
dakinsa, shikuma sai ya bita, ya
dan ja kofa ahankali ya dinga
shafata tanajin dadi, tun tana
zizzilewa har yau-da-gobe ta
saba tasaki jiki da ita,shikenan
tasamu gurin zuwa, watarana
ma sai taqi zuwa tallan taje
dakinsa suyi lalata shikuma yayi
mata juye, abin nufi ya biya kudin
duk
Title :
YAR TALLA......
Description : Daga Hamisu Hassan Ahmed A kasar hausa duk inda kaji ance 'Yar Talla to ana nufin wata mace wacce take dauko kayan siyarwa take yawo...
Rating :
5