Babban Muftin kasar Sa'udiyya, ya yi kakkausar suka a kan kasar Iran, yana cewa 'yan kasar ba Musulmi ba ne.
Babban Muftin, Abdulaziz Al Sheikh ya bayyana Iraniyawan a matsayin wadanda ke da alaka da addinin Zorosta, wanda ke da karfi a kasar gabanin Musulunci.
Kalaman Muftin sun biyo bayan kakkausar da Ayatullahi Ali Khamenei ya yi wa Sa'udiyyar a kan yadda take gudanar da sha'anin aikin hajji.
Ayatullahi Khamenei din ya zargi hukumomin Sa'udiyya da kisan masu ibadar da turmutsutsin da aka yi a bara ya halaka.
Title :
Yan Iran Ba Musulmai Bane - Saudiyya
Description : Babban Muftin kasar Sa'udiyya, ya yi kakkausar suka a kan kasar Iran, yana cewa 'yan kasar ba Musulmi ba ne. Babban Muftin, Abdulaz...
Rating :
5