Gwamnatin Tarayya ta zargi wasu da amfani da ‘Yan matan Chibok a matsayin dama ta samun kudi domin Kan su. Wasu Kungiyoyi masu zaman kan su suna amfani da sunan ‘Yan matan na Chibok da aka sace wajen neman kudi a Kasar Amurka yayin da wasu ke jimamin bacewar ta su.
Premium Times ta rahoto cewa Ma’aikatar harkokin mata ta Kasar ta zargi wasu Kungiyoyi da yin amfani da ‘Yan matan Chibok da Boko Haram suka sace a matsayin hanyar cin abinci. Haka kuma wasu dai daga cikin iyayen ‘Yan matan na Chibok da aka sace sun zargi wasu Kungiyoyi da yin amfani da sunan su kawai don su samu kudi.
Ministar harkokin mata ta Kasa, Aisha Alhassan Jummai tace mutane na karbar kudi da sunan Matan Chibok. Ta bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ta tattauna da iyayen matan da aka sace a Garin Maiduguri, na Jihar Borno. Ministar ta ce wasu mutane na samun kudi da sunan wasu daga cikin matan da aka kai Kasar Amurka suyi karatu. Idan ba a manta ba, an kai wasu matan na Chibok da suka kubuta daga hannun Boko Haram zuwa Amurka karatu, wannan ya ba wasu damar karbar kudi da sunan ‘Yan Matan.
Ministar tace Gwamnati za ta dubi wannan batu da idon gyara, don yanzu haka, ‘Yan mata 5 ne kadai a Amerikar, bayan kuwa an yi alkawarin daukar nauyin su 15. Ministar tace za a gana da iyayen wadannan yara, duk da cewa wasu masu zaman kan su ne suka dauki nauyin tafiyar ta su, Gwamnati ba za ta cigaba da zura idanu ba.
Wata daga cikin iyayn mai suna Yakubu Nkeki Maiva tace, suna so Gwamnati ta dauki dawainiyar wannan harkar, ba a kyale wasu mutane can ba.