Wani magidanci ya yi wa wata ’yar shekara 9 fyade har ta mutu a Unguwar Rigasa a karamar Hukumar Igabi a makon jiya.
Aminiya ta samu labarin cewa wanda ake zargin wanda ya haura shekara 50, ya yi wa yarinyar fyade ne a lokacin da ta je sayen madara da wani makwabcinsu ya aike ta ta sayo masa.
Mahaifin yarinyar Abdullahi Ibrahim, cikin tashin hankali ya ce yana ganin wanda ake zargin ya tare yarinyar ce a kan hanyarta ta zuwa sayo madarar. “Bayan ya yi mata fyade sai ya bar ta, ta yi ta zubar da jini, wanda haka ya yi sanadin rasuwarta. Wani yaro dan shekara uku da ne ya ce ya ga marigayiyar da mutumin. Kuma da farko da aka tambaye shi sai ya musanta haka, amma daga bisani ya amince ya aikata laifin,” inji shi.
Tuni an soma bincike kan wanda ake zargin, ita kuma marigayiyar tuni aka binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Wannan lamari yana zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i yake neman a rika daure masu fyade rai-da-rai tare da hukunci mai tsanani a jihar.
kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Aliyu Usman ya ci tura domin bai amsa wayarsa ba.
A wani labarin kuma mazauna Unguwar Kakuri, Kaduna a ranar Litinin da ta gabata ’yan fashi sun hallaka shugaban ’yan sintiri na yankin. dan sintirin mai suna Buhari Ahmadu Tanko ya rasa ransa ne da misalin karfe 3:00 na dare a harabar Kamfanin Masakar Arewa da ke unguwar. Bayanai sun ce ’yan fashin sun yi artabu a cikin masakar lokacin da suka shiga da nufin yin sata.
Aminiya ta samu labarin cewa marigayin ya rasu ne a lokacin da barayin suka doka masa karfe a kai. Kuma kashe shugaban ya tayar wa abokan aikinsa hankali inda suka yi gungu suka far wa gidajen iyayen yaran da suke zargi da hannu wajen kashe shugaban. Akalla a kona gida daya da mota da wasu kayayyaki da ake tsammanin na dangin wadanda ake zargin ne.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Aliyu Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce barayin su kusan 20, sun far wa ’yan sintirin inda suka kashe shugaban.
Tuni ’yan sanda suka kaddamar da bincike domin gano masu hannu a kashe shugaban, wanda aka binne shi a makabartar Tudun Wada da misalin
Source Aminiya Hausa