A daidai lokacin da al'ummar Musulmi ke shirye shiryen bikin babbar Sallah, teloli a jihar Adamawa sun koka da rashin ayyukan dinkin Sallah, telolin dai sun ce masu kai dinkunan Sallah sun ragu da kashi 70 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarun da suka wuce.
Salihu Abubakar wani tela ne a kasuwar shoping complex dake Yola, ya kuma shaidawa Zuma Times cewa yana zuwa aiki ne kawai amma tamkar ba dinkunan Sallah yake yi ba, ya kara da cewa rashin kudi a hannun ya talakawa na daga cikin abin da ya haifar da wannan al'amari.
Karayar tattalin arzikin Nijeriya dai yana tasiri akan al'ummar kasar, ko da yake gwamnati ta ce tana kokarin samar da hanyoyin da za su farfado da tattalin arzikin kasa.
Yaya al'amarin yake a wuraren ku?
Zuwa Times Hausa