Daya daga cikin jerin 'yan Boko Haram din da rundunar sojojin Nijeriya ke nema ruwa a jallo, wato Muhammadu Bulama wanda yake lamba na 105 a jerin wadanda ake neman ya shiga hannu a jiya Talata, inda aka kama shi a jihar Yobe.
An kama Bulama ne tare da wasu mutane biyu da ake zargin su ma membobin kungiyar Boko Haram ne masu suna Ardo Abba Muhammed, wanda ya bayyana cewa shi yaya ne shi ga Bulama da kuma Muhammadu Kaigama, wadanda aka kama su tare da taimakon 'yan bangan yankin Azare dake karamar hukumar Gujba a jihar ta Yobe.
An kama sune a yayin da suke kan doki, inda suke ingiza keyar wasu tumaki zuwa kasuwa domin sayarwa.
A yayin bincike Bulama ya tabbatar da cewa hotonsa ne a cikin jerin 'yan Boko Haram din da sojoji suke nema, sannan kuma ya kara da cewa aikin sa shine yi wa 'yan Boko Haram safarar dabbobi.
Bulama ya kuma da cewa sun fito gari ne domin sayar da dabbobin kasancewar kudi ya yi musu karanci a inda suke boye, sannan kuma za su nemi kayan abincin da za su yi bikin sallah da shi.