....ya kuma rantsar da sabbin kwamishinonin jihar
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya rantsar da sabuwar kwamishiniyar harkokin mata ta Jihar Kano, Hajia Yardada Maikano Bichi a fadar Gwamnatin jihar,
Hajiya Yardada Maikano dai ta maye gurbin Barrister Zubaida ne wacce aka sauya zuwa Kwamishiniyar tsara kasafin kudi da tsare-tsare a yayinda ita kuma tsohuwar kwamishiniyar kasafin, Hajia Aisha Bello aka nada ta mukamin Akanta Janar.
Gwamnan ya rantsar da kwamishiniyar ne a jiya Laraba gabanin soma gudanar da taron majalisar zartarwar jihar, Misis Aisha Bello ita ce mace ta farko a jihar Kano da zata rike mukamin Akanta Janar.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin fadar Gwamnatin jihar, Salihu Tanko Yakasai ya ce a zaman majalisar na jiya, Gwamna Ganduje ya kuma sanya hannu kan dokar biyan harajin filaye wacce majalisar jihar ta gabatar masa a kwanakin baya.
Sanarwar tace sabuwar dokar zata bunkasa kudaden shiga da jihar ke samu a inda darajar jihar zata tashi daga Matsayin jiha ta 10 zuwa jiha ta Biyu a samun kudaden shiga bayan jihar Lagos.
Gwamnan ya kuma yiwa majalisar bayani akan ziyarar mako guda da yakai kasar India karkashin gayyatar kamfanin Skipperseil. Yace makasudin ziyarar tashi shine halartar kaddamar da tashar wutar lantarki da kamfanin yayi, sannan kuma ya gana da dalibai yan asalin jihar Kano dake karatu a kasar.
Yana mai cewa ya kuma sanya hannun kan wasu yarjejeniyoyi da masu zuba jari a kasar ta India a fannin Noma da Lafiya da Makamashi.