Yan Fim Sun Tallafawa Tsohon Abokin Sana'arsu, Daudu Galadanci
*Wannan Shine Karon Farko Da Na Soma Ido Hudu Da Daudu Galadanci, Inji Hadiza Gabon
A yammacin jiya ne wasu daga cikin 'yan fim suka kai ziyara gidan tsohon dan fim din nan, Malam Daudu Galadanci.
A yayin ziyarar 'yan fim din sun tallafa masa da kayan abinci da kudi.
Daga cikin 'yan fim din da suka kai masa ziyara sun hada da furodusa Usman Mu'azu, Yunusa Mu'azu, Hadiza Aliyu Gabon da sauransu.
Jaruma Hadiza ta bayyana cewa wannan shine karo na farko da ta soma yin ido hudu da Dattijon, wanda ya kai kusan shekaru arba'in ana damawa da shi a masana'antar fim.
A yayin jin ta bakin Furodusa Usman Mu'azu da RARIYA ta yi game da ziyarar da suka kaiwa Dattijon, ya bayyana cewa sun kudiri aniyar tallafawa Malam Galadanci ne kasancewarsa wanda karfin sa ya gaza a yanzu saboda tsufa da ya yi, domin a kalla ya kai shekaru 87 a duniya.
Usman ya kara da cewa shi da Jaruma Gabon suna kan shirya wata Gidauniya domin tallafawa tsoffin 'yan fim irin su Kasimu Yero, Samanja, Malam Waragis, da kuma iyalan wasu 'yan fim da suka rasu kamar su Baffa Ahmad Cinnaka, Dan Wazan, Goloko da sauransu.
Rariya
Title :
Photos: Hadiza Gabon Ta Ziyarci Tsohon Abokin Sana'arsu, Daudu Galadanci
Description : Yan Fim Sun Tallafawa Tsohon Abokin Sana'arsu, Daudu Galadanci *Wannan Shine Karon Farko Da Na Soma Ido Hudu Da Daudu Galadanci, Inji H...
Rating :
5