*TAMBAYA*
Assalamu alaikum Malam dan Allah me ya dace mace tayi gobe idan tana haila dan samun lada. ??
*AMSA*
Wa'alaikumus Salaamu wa rahamatullaahi wa barakaatuh.
*Idan mace ta saba yin azumin Nafila sai ta wayi gari a ranar Arfa tana
cikin jinin al'ada, Toh Tabbas zata Samu ladan Azumin Arfa*
Domin akwai hadisin da yake nunawa duk wanda ya kasance yana yin wata
ibada sai rashin lafiya ta sa bai samu yayi ba, toh za'a rubuta masa
cikakken lada.
*Amma idan bata saba yi ba toh ga abin da zata yi Qila ta samu lada kamar ladan mai azumi, gasu kamar haka*:-
1) Ta yawaita Tasbihi
2) Ta yawaita Hailala
3) Hamdala
4) Istigifaari
5) Salatin Annabi
6) Karatun al-Qur'ani (Duk da kasancewar malamai sunyi sa6ani dangane
da karatun al-Qur'ani ga mai haila, amma zance mafi inganci shine ya
halarta mai jinin haila ta dauki al-Qur'ani)
7) Sadaka da taimakawa masu rauni
8) Yawan ambaton Allaah (Zikiri) etc
Manzon Allaah swallallaahu alaihi wa sallam yace:-
Mafi alkhairin abin da na fada ni da annabawan da suka gaba ceni a ranar arfa shine:
لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير.
Allaah shine mafi sani.
Source zuma Times Hausa
Title :
Me Ya Kamata Mai Haila Tayi A Ranar Arfa
Description : *TAMBAYA* Assalamu alaikum Malam dan Allah me ya dace mace tayi gobe idan tana haila dan samun lada. ?? *AMSA* Wa'alaikumus S...
Rating :
5