.
ANNABI (S.A.W) ya bamu labarin cewa A lokacin da yaje
"Mi'iraji" ya leka cikin wuta, Sai yaga wasu Mutane Tsirara,
an tattarasu a cikin wani Ramin Dagwalon Azaba Wuta tana
ci ta Qasansu,
.
kuma Mala'iku Suna Jibgarsu suna ci gaba da Musu
Azaba.
.
Sai ya tambayi "Mala'ika Jibrilu Yana Cewa "YA JIBRILU
WA'DANNAN SU WAYE NE?"
.
Sai Jibril Yace "WADANNAN MAZINATA NE".
.
ANNABI (S.A.W) ya bada Labarin cewa akwai wani irin
"IHU" da kururuwa wanda 'Yan wuta suke yi an bude musu
Farjojin Mazinata.
.
Kunji fa Jama'a, Saboda tsananin wari da 'doyin Al'aurar
Mazinata, idan an budeshi sai dukkan 'Yan wuta suyi ta
"IHU" suna ta Yin kururuwa.
.
Hakanan akwai wani Ruwa Mai Bala'in wari wanda yake
fitowa daga cikin Al'aurar Mazinata idan ana gana musu
Azaba.
.
Wannan Ruwan Sunansa "TEENUL KHABAAL".
.
Yana daga cikin Nau'in Abincin da 'Yan Wuta suke ci A
Cikin Wuta
.
Ya ku Jama'a ina Bamu Shawara dacewa
mu Guji Zina da dukkan Dangoginta, Wallahi Zina Bala'i ce
Tun Anan duniya Ballenta ma a Can lahira.
.
Ya Allah ka Tsaremu kuma ka Tsare Farjojin mu daga
Aikata Mummunar Kaba'ira Bijahi S.A.W