Rahotanni daga kasashen Asiya inda dillalan Nijeriya ke sayo shinkafa sun koka kan rashin ciniki sakamakon matakin ga gwamnatin tarayya ta dauka na hana shigo da shinkafar.
Ma'aikatar ciniki na kasar Thailand ta nuna cewa cinikin shinkafa ya ragu da kusan kashi 23 a cewarta, a farkon shekara kasar ta sayar da tan milyan 3.6 amma a watan da ya gabata, ta iya sayar da tan 700 ne kacal. Rahotanni sun tabbatar da cewa kusan duk manoman kasashen na Asiya suna fuskantar wannan matsala.